African Dish: Awara with sauce
Awara with sauce Ingredients
1
Waken awara.
2
Mai.
3
Magi.
4
Tattasai.
5
Tarugu.
6
Albasa.
7
Ruwan yami/tsagaro/jikkakar tsamiya.
Cooking Guidances
Step 1
Zaki wanke waken awarar ki Gyara da kyau ki kai markade.
Step 2
Idan aka markado saiki tace ki saka a tukunya.
Step 3
Ki daura a wuta idan ya tafaso(ya boro)saiki saka ruwan yamin ko alif ko ruwan tsamiya.
Step 4
Haka zakiyi har saiya hade madar ta cire yayi gumba.
Step 5
Saiki kwashe ki saka a buhu ko mataci ruwan su fita.
Step 6
Saiki yayyanka ki jika ruwan magi kisa a awarar.
Step 7
Saiki aza mai a wuta idan yayi zafi saiki soya awarar.
Step 8
Saiki jajjaga tattasai da tarugu da albasa kuma ki yayyanka albasa.
Step 9
Kisa mai a tukunya ki saka jajjagen kisa magi.
Step 10
Saiki sa sauce din akan awarar.
Post navigation